Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana mamakinsa kan ganin yanda wasu mutanen Zamfara ke son ya ci gaba da zama gwamnan jihar.
Wata kungiya me suna Zamfara Decides ce ta kaiwa Gwamna Matawalle fom din takarar gwamna na Miliyan 50 inda tace tana goyon bayan ya sake tsayawa takarar gwamnan jihar.
A martaninsa ta bakin me magana da yawunsa, Zailani Bappa, Gwamna Matawalle ya bayyana cewa, yayi farin ciki da hakan.
Kuma yayi mamakin yanda mutane ke son ya ci gaba da zama gwamnan jihar Zamfara inda yace ba zai basu kunya ba.