Tsohon Shugaban Kasa na mulkin Soja, Yakubu Gowon ya bayyana cewa ya yi nadama kan yadda bai yi amfani da ikonsa a lokacin yana Shugaban kasa ba wajen mallakar fili a Babban birnin tarayya Abuja duk da yake shi fara tunanin mayar da garin fadar gwamnatin tarayya.
Gowon ya ce, gwamnatocin da suka gabace shi, ba su yi la’akari da wannan kokari nasa ba sai da ya kai kuka wajen Tsohon Shugaban Kasa, Ibrahim Badamasi kan ko titi guda a birnin ba a sanya sunansa a kai ba. Ya ce a lokacin yana da ikon mayar da mahaifarsa ta garin Jos a matsayin birnin tarayya amma kuma ya ki yin haka don gudun kada a zarge shi da kabilanci.
rariya