fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Nafisa Abdullahi tace ta daina Fitowa a cikin shirin labarina

Tauraruwar fina-finan Hausa,  Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa, ta daina fitowa a cikin shirin Labarina.

 

Nafisa ta bayyana hakane a wata wasika data aikewa kamfanin Saira Movies.

 

Nafisa tace tana Alfahari da shirin Labarina duk inda take kuma alakarta da kamfanin Saira Movies tana nan amma ba zata iya ci gaba da fitowa a shirin ba.

 

Ta bayyana dalilan Karatu, da Maida hankali kan fim dinta da take shiryawa da kuma wasu sauran dalilai da suka sa ta yanke wannan shawara.

Karanta wannan  Mai kudin Duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na kamfanin Telsa, shin ko meye dalili?

Ta kuma kara da baiwa masoyanta hakuri.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.