Davido ya biya darakta Miliyan 100 na Farko aiki da shi kan bediyon waka.
Mawakin Afrobeats na Najeriya, Davido, ya bayyana cewa; ya kashe Naira miliyan 100 a wani faifan bidiyo na waka da TG Omori ya jagoranta.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan rediyon Beats 99.9 fm a baya-bayan nan, yayin da yake magana kan sabon kundin sa mai suna TIMELESS.
Davido ya ce ya yi farin ciki da aikin da Omori ya gabatar kuma ya lura cewa kudin shine N100m na farko da yaron daraktan zai karba daga hannun kowane mai fasaha.