fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Najeriya ba zata taba samun cigaba ba dole sai an samu canjin gwamnati, cewar Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa Najeriya ba zata taba samun cigaba ba dole sai an samu canjin shuwagabanni an sake ginata.

Mataimakinsa Ifeanyi Okowa ne ya bayyana hakan bayan ya wakilcesa a taron kara karatun Injila na shekara da Kiristoci ke gudanarwa wanda aka yi jiya a jihar Ekiti.

Okowa yace Najeriya na Bukatar jajirtattun shuwagabanni wa’yanda zasu tashe tsaye su taimakawa talakawa dama sauran al’ummar kasar bakidaya.

Inda yace saboda haka dole idan har ana so wannan abin ya faru sai an sauya gwamnatin kasar domin a kawo wadda zatayi aiki tukuru ta warware matsalolin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.