fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Najeriya babu isassun jami’an tsaro, ku tashi ku kare kanku>>Gwamnan Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya bayyana dalilinsa na yin kira ga al’ummar jiharsa da su nemi makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a Katsina wanda aka yaɗa kai tsaye ta kafar Facebook, ya ce dole ne al’umma su tashi tsaye domin babu isassun jami’an tsaron da za su kare su.

Masari ya rika amsa tambayoyi daga manema labarai a yayin wannan taro, kuma cikin tambayoyin da aka masa har da wadanda suka shafi harkokin tsaro.

Ya yi iƙirarin cewa an samu sauƙi a jihar Katsina duk da cewa abubuwa sun tsananta a Jihar Sokoto cikin kananan hukumomi guda biyu.

Gwamnan wanda a baya yake ɗa’awar sulhu da ƴan bindiga kafin ya yi watsi da manufar, ya ce ‘yan sandan da ke jiharsa ba su kai 3,000 ba, yana mai cewa gwamnati za ta taimaka wa masu son mallakar makaman don taimaka wa harkar tsaro.

“Harkar tsaron nan ta kowa da kowa ce babu bambancin siyasa – abin da mutane ya kamata su sani shi ne a Katsina ba ka da ‘yan sanda 3,000…saboda haka muke kira ga duk wanda zai iya ya nemi makami ya kare kan sa da iyalansa,” in ji Gwamna Masari.

Ya ci gaba da cewa: “Shari’ar Musulunci ma ta yarda mutum ya kare kan sa da dukiyarsa da iyalansa. Idan ka mutu kana ƙoƙarin kare kanka ka yi shahada. Abin baƙin ciki ma shi ne ta yaya ‘yan fashi za su samu bindiga amma mutanen kirki ba su da ita da za su kare kansu da iyalansu.”

Masari ya ce idan ka zuba sojojin Najeriya gaba daya a dajin Zamfara za su bace ne domin yawansu ba zai iya game dajin ba baki daya, don haka dole a hada karfi da karfe a kare kai baki daya.

Sai dai gwamnan ya soki ayyukan ‘yan sa-kai (‘yan banga), yana mai cewa “ba mu yarda da aikin ‘yan sa-kai ba saboda ƙaura suke yi daga garinsu zuwa wani gari, mun fi son mutane su kare garuruwansu da kansu”.

Ya ce akwai bukatar komawa baya a fahimci menene ya fara jawo wannan matsalar ta tsaro da haka ne kawai za a iya lalubo bakin wannan matsala da ta gagarin kwandila.

Ya yi suka ga masu zanga-zanga musamman wadanda suke hawa titina su rufe hanya, su hana al’umma harkokinsu na yau da gobe.

Inda ya kalubalanci wadanda ke hakan da indai mazaje ne su, “lokacin da aka yi kuruwa su fito domin kare jiharsu da iyalansu”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.