fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Najeriya na bukatar addu’a>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da addu’a dan samun zaman lafiya a kasa baki daya.

 

Shugaban yayi maganar ne a wajan bikin kadiriyya na shekaru 70. Ministan Noma, Sabo Nanono ne ya wakilci shugaban kasar a wajan bikin inda yace Addu’a zata taimaka wajan hadin kai da kuma zaman lafiya.

Shugaban ya kuma jawo hankalin matasa da su yi amfani da tallafin gwamnati daban-daban da ake gudanarwa wajan koyan sana’o’in da zasu dogara da kansu.

 

Shugaban ya kuma jinjinawa shugaban Kadiriyya, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara.

Leave a Reply

Your email address will not be published.