Gwamnan jihar Rivers, kuma me son tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023, Watau Nyesome Wike ya bayyana cewa idan PDP ta bashi rikitin tsayawa takarar shugaban kasa, to lallai zai iya lashe zaben.
Wike yace irinshine Najeriya ke bukata ya zama shugabanta saboda gaskiya.
Yace Najeriya na bukatar shugaba wand baida boye boye duk abinda ya gani zai yi magana akansa.
Wike ya bayyana hakane yayin da yake ganaw da wakilan PDP a jihar Naija a ci gaba da neman kuri’ar wakilan jam’iyyar da yake da zasu yi zaben fidda gwani.
Wike yace idan aka nemi tsayar da dan takara na bai daya, hakan ba matsala bane muddin an yi gaskiya a ciki.
Yace idan ya zama shugaba kasa, zai tabbatar ya samar da tsaro sanoda gwamnati me ci bata samar da tsaro yanda ya kamata ba.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ya ruwaito Wike na cewa amma koda ba shine aka zaba a matsayin wanda zai zama dan takarar jam’iyyar PDP ba zai goyi bayan kungiyar.