fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Najeriya na cikin manyan kasashe 10 dake safarar mutane da muggan kwayoyi – Rahoto

Kididdigar laifuffuka ta Duniya ta 2021 ta sanya Najeriya cikin manyan kasuwanni 10 na laifukan fataucin mutane, bindigogi, kwayoyi, da kuma sauran laifuka.

Kididdigar ta nuna cewa kasashen da suka fi fuskantar manyan laifuka su ne wadanda ke fama da rikici ko kuma tawaya, inda ta kara da cewa irin wadannan kasashen da abin ya shafa sun fi fuskantar manyan laifuka.

Rahoton ya ce Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ce ke kan gaba a jerin masu aikata laifuka da maki 7.75, sai Columbia da maki 7.66; Myanmar 7.59; Mexico 7.56; Najeriya 7.15; Iran 7.10; Afghanistan 7.08; Iraki 7.05; Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya 7.04 da Honduras 6.08.

Sauran kasashen da suka fi samun maki sun hada da Afghanistan, Iraki da Syria, inda tashe-tashen hankula suka durkusar da tattalin arzikin kasar, wanda ya kai ga gudun hijira da kuma kwararar makamai.

Karanta wannan  Kotun Landan ta sake daga shari'ar Ekweremadu da matarsa, tace laifin safarar sassan jikin dan adam ba karamin laifi bane

Cibiyar Nazarin Tsaro da INTERPOL ce suka rubuta rahoton dangane da Ƙaddamar da Laifukan Tsare-tsare na Ƙasashen Duniya.

Ƙasashe mafi karanci da mafi kyawun juriya da aminci na zamantakewa sun haɗa da Tuvalu 1.54; Nauru 1.76; Sao Tome & Principe 1.78; Liechtenstein 1.88; Samoa 2.04; Vanuatu 2.20; Tsibirin Marshal 2.31; Kiribati 2.35; Luxembourg 2.36 da Monaco 2.43.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.