fbpx
Friday, February 26
Shadow

Najeriya na fuskantar matsalar Karancin Abinci Saboda kasashen da take siyo Abincin sun fara boyeshi

Matsalar manyan kasashen Duniya dake ta kokarin tara Abinci na wa Najeriya da sauran kasashen da suka dogara da shigo da Abinci daga kasashen waje Barazanar yunwa.

 

Zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 yasa kasashen da suka ci gaba ke ta kokarin yin tanadin Abinci saboda rashin tabbas na me zai faru nan gaba.

 

Hakanan hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet ta bayyana cewa matsalar sauyin yanayi da kuma ta tsaro na barazana ga manoma ta yamda da wuya a samu yawan abincin da ake so.

 

Abincin da ake tsammanin zai yi wahala ashine Masara, Alkama, Shinkafa da sauransu, Kamar yanda Guardian ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *