fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Najeriya na tsaka mai wuya dole gwamnati ta sake daure damara, cewar kungiyar Kiristocin Najeriya

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta sashen Arewa ta bayyana bacin ranta kan matsalar tsaron da kasar ke fama dashi musamman a yankin Arewa.

Inda tace Najeriya na tsaka mai wuya domin ‘yan bindiga sun matsawa kasar sosai da kashe kashe da kuma garkuwa da mutane bakidaya.

Kungiyar ta kara da cewa ana fuskantar wannan matsalar ne musamman a jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Niger, Benue, Plateau, Taraba, Kebbi, Sokoto hadda ma babban birnin tarayya Abuja.

Kuma wannan matsalar har ta kai ga ‘yan bindigar na cewa zasu yi garkuwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, saboda haka ya kamata gwamnati ta tashi tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published.