fbpx
Monday, August 15
Shadow

Najeriya sai ta kone kurmus idan ta bari Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa, cewar mai sharhin labaran siyasa

Dan Najeriya dake sharhi akan siyasa, Reno Omokri ya bayyana bacin ransa akan hayar fastocin bogi da Tinubu yayi a taron kaddamar da Kashim Shettima a matsayin abokin takararsa.

Inda ya bayyana cewa Dan takarar shugaban kasar na APC mayaudari ne kuma ya hayo fastocin ne don ya yaudari Kirista su zabe shi.

Inda Omokri ya kara da cewa idan har dan takarar jam’iyyar APC yayi nasarar cin zaben shekarar 2023 to babu shakka Najeriya konewa zatayi kurmus.

Har yanzu dai ana cigaba da cece kuce musamman ta fannin Kirista kan zabar Musulmi da Tinubu yayi a matsayin abokin takararsa na zaben shugaban kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published.