fbpx
Tuesday, December 1
Shadow

Najeriya ta fada matsin tattalin arziki mafi Muni cikin shekaru 30 da suka gabata

Rahotanni da aka yi amfani da alkaluman tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya ta fada matsin tattalin arziki mafi muni a cikin shekaru 30 da suka gabata.

 

Kididdigar tattalin arziki da hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta fitar sun nuna cewa tattalin arzikin ya samu nakasu da kaso 3.62 a cikin watanni 3 da suka gabata.

A karo na 2 kenan ana samun raguwar karfin tattalin arzikin Najeriya a shekarar 2020 wanda rabon a ga haka tin shekarar 2016.

 

Jimullar raguwar kargin tattalin arzikin a yanzu ya kai kaso -2.48. Rabon da aga irin wannan karayar tattalin arziki tun shekarar 1987 wanda ya samu raguwa a wancan lokaci da kaso 10.8.

 

Bankin Duniya ya bayyana cewa wannan ne karo na 2 da Najeriya ta fada matsin tattalin arziki a karkashin Mulkin Dimokradiyya na shugaban kasa,  Muhammadu Buhari sannan kuma karo na 4 a matsayin da yake shugaban kasa.

 

A baya dai bankin Duniyar yayi gargadin cewa kasar zata fada irin wannan yanayi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Aiko mana da labarin wani abu da ya faru a gabanka, Zamu biyaka: Send us eyewitness report we will pay youLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *