fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Najeriya ta kashe sama da naira triliyan hudu kan sayan jirage sama da makaman yaki amma ‘yan bindigar dake kawo hari akan babura sun gagareta, cewar Shehu Sani

Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyan cewa Najeriya na cikin wani mawuyacin hali kuma tan bukayar agajin gaggawa.

Inda yace hare haren da aka kaiwa ofisoshin gwamnati da makarantu da gidan yari sun nuna cewa wasu ne ke son kwance kasar.

Inda yace Najeriya na bukatar jajirtaccen shugaba wanda zai iya magance mata matsalar rashin tsaro.

A karshe yace Najeriya ta kashe sama da triliyan hudu cikin shekaru bakwai don sayen makamai hadda jiragen saman na yaki, amma yan bindigar dake hari a babura sun gagareta.

Leave a Reply

Your email address will not be published.