fbpx
Monday, March 1
Shadow

Najeriya Ta shigo da Alkama Ta Kimanin Naira Tiriliyan 2.2 Cikin Shekaru 4>>Ministan Noma

Najeriya ta shigo da alkama na Naira tiriliyan 2.2 a cikin shekaru hudu wanda gwamnati ta yi, Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono ya bayyana.
Nanono, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban bako a lokacin bikin ranar manoman alkama a Kano, ya damu da karancin noman alkama a Najeriya duk da yawan bukatarta.
Ya bukaci gwamnonin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noman alkama da su saka jari a ayyukan noman rani ta yadda za a mayar da noman alkama abin birgewa da kuma gasa kamar na shinkafa.
Kungiyar Masu Hada Fulawa ta Najeriya (FMAN) a wajen taron ta ce ta fara shirin fitar da wani shiri don karfafawa manoman alkama 800 a Jihohin Kano, Jigawa da Kebbi.
Tsarin zai hada da rancen bada tallafi da horo kan dabarun noman zamani ga manoma da nufin bunkasa abinda suke fitarwa a kowace shekara tare da rage farashin kayan masarufi.
Shugabar FMAN, Shirin Raya Alkama, Sarah Huber, ta ce: “Muna fadada sayenmu a matsayin masana’antu a fadin jihohin da ke samar da alkama ta hanyar karin hadawa da karfin rumbunan adana kayayyaki, gami da kudurin samar da duk hatsin alkama da ya dace da matsayin ingantaccen tsari . ”
Ta ce babbar manufar ita ce ta sanya alkama ta zama mai gogayya da shinkafa da sauran noman rani, lura da cewa an kafa cibiyoyin kula da manoman alkama a kananan hukumomi 15 a Jihohin Jigawa, Kano da Kebbi don gudanar da noman alkama a shekarar 2020/2021.
Huber ta kuma ce cibiyoyin za su bayar da horo kyauta ga manoma kan hanyoyin noman zamani sannan kuma za su kasance matattarar kai tsaye na alkama ga manoma 5,000.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *