Rahotanni sun bayyana cewa, Najariya ta tafka asarar Biliyan 500.6 na danyen man fetur.
Asarar ta farune a tsakanin watan Janairu zuwa Mayu.
Kuma dalili shine rashin fitar da yawan danyen man da ya kamata ace Najeriya na fitarwa.
A baya dai Najariya na fitar da gangar danyen mai miliyan 43.369 duk wata amma a tsakanin watan Janairu da Mayu ta fitar da jimullar ganga miliyan 11.63.
Rahoton da punchng ta kawo tace Najariya na ci gaba da asarar kudi saboda raguwar yawan danyen man da take fitarwa.