fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Najeriya ta zamo babban birnin ‘yan ta’adda, cewa Fani Kayode

Tsohon ministan dake lura da harkar jitagen sama, Fani Kayode ya bayyana cewa ya fara gajiya da matsakar tsaron dake damun kasa Najeriya.

Kayode ya kasance dan jam’iyyar APC amma yace yanzu haren haren da aka kaiwa a kasar yasa Najeriya ta zamo babbar kasar ‘yan ta’adda.

Ya bayyana hakan ne biyo bayan kaia tagawar tsaro ta Buhari da kuma harin da aka kaiwa gidan yari na Kuje, sannan gashi an kashe sojoji a jihar Niger da kuma hare haren da ake cigaba da kaiwa majami’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published.