fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Najeriya tafi kasashen Amurka da na Turawa, an fi aikata laifi a wadancan kasashen>>Lai Muhammad

Ministan yada labarai, Lai Muhammad ya bayyana cewa, Najeriya ta fi kasashen Amurka da na turawa inda yace an fi aikata miyagun laifukan wadancan kasashen.

 

Yace an fi aikata fyade da kuma zakkewa ‘yan uwa da danginsu ke yi a kasashen Turawa da Amurka fiye da Najeriya.

 

Yace a Najeriya akwai al’ada da kuma addini dake hana mutane aikata irin wadannan miyagun laifukan, ya yi kira ga iyaye da su rika nunawa ‘ya’yansu muhimmancin al’ada da kuma abubuwan da bai kamata su aikata ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.