fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

Najeriyace kasa ta daya da zataje da ‘yan wasa mafi karancin shekaru buga kofin Duniya

A wata kididdiga da hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA tayi da hadin gwiwar wani shafin yanar gizo me yin sharhi da fitar da cikakkun bayanai akan harkar kwallon kafa ta Duniya me suna CIES a takice, sun bayyana cewa a cikin kasashen Duniya da suka bayyana sunayen ‘yan kwallon da zasu je kasar Rasha dasu dan buga musu gasar cin kofin kwallon Duniya, Najeriyace kasar da taje da ‘yan wasa mafi karancin shekaru.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Kididdigar wadda akayi ta nuna Najeriya amatsayi na Daya a Duniya da taje da ‘yan wasa masu shekaru matsakaitan shekaru sannan sai kasar Jamus sai Ingila sai Denmar dadai sauransu kamar yanda ake iya gani a cikin wannan hoton nasama.

Haka kuma kididdigar tayi bincike akan kasashen da sukaje da’yan wasa masu tsawo, inda Kasashen Peru, Argentina, Uruguay, Saudi Arabia, JApan, Mexico da Sapain ne sukaje da ‘yan wasan da suka fi tsawo.
Muna fatan ‘yan wasan na Najeriya zasu nuna kazarkazar irin na matasan su tabuka abin azo a gani lokacin buga wasan.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Tura ta kai bango: kalli bidiyon yanda 'yan Inyamurai suka fara kama 'yan IPOB suna kashewa

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.