Wednesday, December 4
Shadow

Namijin Goro: Namijin goro karfin maza


Namijin Goro sanannen abune da ake amfani dashi a duka fadin Duniya. Akan yi amfani dashi wajan warkar da cutar Mura ko cutar Koda.

Namijin goro in English

Sunan namijin goro da turanci shine Bitter Kola, ana kuma ce masa Bitter Cola, ko kuma Garcinia Kola.

Ana samun Namijin goro a kasashen Afrika kamar su Gambia, Democratic Republic of the Congo, Ivory Coast, Mali, Gabon, Ghana, Liberia, Nigeria, Senegal da Sierra Leone.

Kuma masana sun yi bayani sosai akan amfanin da yakewa jikin dan Adam kamar yanda zamu gani a kasa.

Amfanin namijin goro

  • Namijin goro na taimakawa masu son rage kiba
  • Yana taimakawa sarrafa abinci.
  • Yana taimakawa garkuwar jiki.
  • Yana saukar da hawan jini.
  • Yana maganin bacin rai da damuwa.
  • Yana maganin guba.
  • Yana maganin ciwon ido.
  • Yana maganin zazzabin Malaria.
  • Yana karawa namiji kuzarin mazakuta.
  • Yana maganin wasu daga cikin cututtukan da ake dauka wajan jima’i.
  • Yana bada garkuwar kansa.
  • Yana maganin mura.
  • Yana maganin tari.
  • Yana maganin zawo da bacin ciki.
  • Yana maganin ciwon gabobi.
  • Yana taimakawa huhu aiki da kyau.
  • Yana bada garkuwar ciwon suga.
  • Yana taimakawa masu shan taba rage illar tabar.
Karanta Wannan  Amfanin gishiri a gaban mace

Amfanin namijin goro ga maza

Masana sun bayyana daya daga cikin manyan amfanin namijin goro ga maza shine, yana karawa namiji karfin mazakuta.

Masama sun bada shawarar cin namijin goro, kamin a fara jima’i, za’a samu gamsuwa sosai.

Ga sauran amfanin namijin goro ga maza:

  • Yana karawa namiji kuzarin jima’i.
  • Yana karawa marainan namiji nauyi.
  • Yana karawa namiji karfin fitar da maniyyi.

illolin namijin goro

  • Zai iya hana bacci.
  • Zai iya sa jikin mutum karkarwa.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Karanta Wannan  Sunayen Allah (99) Tare Da Fa’idar Kowane Suna Da Kuma Yadda Za A Yi Amfani Da Shi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *