fbpx
Friday, July 1
Shadow

Nan Gaba Kadan Mata (Robots) Za Su Fara Haihuwa>>Scientists Technology

Tun tuni masana suka dukufa wajen samar da injin kyankyasa, inda za a dauki kwayayen halittar namiji da mace a sa a na’ura, sai dai kawai a kira su a ce dan su ya nuna su je su dauka.

To yanzu haka so ake a mayar da shi ga Robots a maimakon inji. A nan za a sanya wa Robot mahaifar roba, ta yadda za ta yi aiki irin na injin nan.

Sai dai har yanzu ba a cimma wannan kudirin ba amma an dukufa wajen bincike, duk da wasu masana suka ce sun samu nasara a kan bera a dakin bincike.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Tottenham ta sayo Richarlison daga kungiyar Everton

Masana suka ce wannan hanya ce da za ta taimaka wa mata don daina daukan ciki da laulayinsa.

Yadda abun zai kasance shi ne daukan biological facts din mutum (kwayoyin halitta da makamantansu) a saka a mahaifar robar Robot din don yin kyankyasa, da zaran lokacin haihuwa ya yi kuma sai ta haihu (kamar a bude cikinta a dauko shi)

—Mohiddeen Ahmad
Scientist, technologist, Founder/CEO of Stackplaza

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.