Kungiyar masu masana’antu na Najeriya, MAN ta bayyana cewa, nan gaba kadan yawan wanda basu da aikin yi zai kai kaso 50 bisa 100 a Najeriya.
Kungiyar tace yanzu yawanci mutane basu da kudi da zasu sayi kayan amfani inda yace yawan kayan amfani da kamfanoni suka samar wanda mutane sun kasa siya, darajarsu ta kai Biliyan 400.
Shugaban Kungiyar, Mansur Ahmed ya shaidawa manema labarai jiya ,Alhamis cewa akwai matsalar rashin kayan aikin da ake sarrafawa Wanda kuma zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 ne ya ta’azzarashi.
Yace masana’antun na bukatar tallafin Gwamnati sannan kuma hukumomi su rage yawan harajin da suke karba.