fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Nan Gwamnati tace zata gina Fim Village mutane suka yi caaaa aka hana amma yanzu zagin ‘yan Fim ake dan basu fito zanga-zanga ba>>Ali Jita

Tauraron mawakin Hausa, Ali Isa Jita wanda yana daya daga cikin kalilan daga masana’antar Kannywood da suka fito zanga-zangar koke kan matsalar tsaro a Arewa ya bayyana cewa har yanzu Arewa bacci take.

 

Jita ya bayyana hakane a wani bayani da yayi kai tsaye ta shafinsa na Instagram wanda wakilin hutudole ya bibiya inda yace tun mawakan da ,irin su Shata sun yi wakar cewa “ku tashi ku farka ‘yan Arewa, kusan bacci aikin kawai ne”

 

Yace amma har yanzu ba’a farka ba. Jita yayi kiran cewa ya kamata a farka, ” An bar Arewa a baya sosai, kudu sun bar Arewa, kamin mu kamasu zamu dauki lokaci me tsawo. Wannan abu dake faruwa ya shafi kowa, wani shi a Arewa idan dai abu ba a gidansu yake ba, kai wani ma ko da a gidansu ake abu idan ba a dakinsu bane to babu ruwansa”

 

Jita ya koka da hassada da rashin sanin ciwon kai da abinda zai amfani kai na mutanen Arewa. Yace yana mamakin abinda yasa gidajen yada labarai basu shiga cikin inda abin ke faruwa suna daukowa suna nunawa mutane irin cikin halin kuncin da mutanen da hare-haren nan ya shafa suke ciki.

 

Yace shekara Aru-Aru haka ake a Arewa, cikin Talauci, yace har ma an saba ganin mutane a cikin wahala ta yanda ba’a damu ba an yadda cewa a ci gaba da rayuwar a haka.

 

Jita yace wallahi idan kaga wani sai ka yi kuka, saboda wahalar rayuwa da yake ciki. Yace amma a haka zaka ga me saida Lemu yana da mata 3, wannan ta haihu waccan ma ta haihu.

Karanta wannan  Dattawan Arewa sun gargadi Atiku cewa kar ya canja Okowa a matsayin abokin takararsa

 

Jita da yake magana kan caccakar da akewa ‘yan Fim saboda rashin fitowa Zanga-zangar ta Arewa yace ” Nan aka kawo maganar gina Fim Village, ba tare da tunanin wane irin ayyuka zai samarwa matasa ba aka yi caaa aka hana gwamnati yi. Amma yanzu wai ana zagin ‘yan fim sun ki su fito a yi zanga-zanga”

 

“Ni wallahi ba dan maganar mutane na fito zanga-zangar ba, saboda ni dan Arewa ne ina da ‘yancin yin hakan sannan saboda ‘ya’yana nan gaba su samu rayuwa me kyau da kuma mutanen da ake kashewa” inji Jita.

 

Jita ya gayyaci Zainab Baba wadda da ita aka fita zanga-zangar shekaran jiya, ta bayyana cewa” Wallahi wannan abu ya shafi kowa, tun ana yi idan ka fita titi a tareka yanzu an fara zuwa har gida a dauki mutum, sai mun tashi tsaye”

 

Jita ya bayyana dalilin da yasa wasu daga cikin abokan aikinsa basu fita suka yi magana ko kuma suka ki shiga zanga-zangar ba.

 

“Kinga ko a cikin mu zaka ji wani wai abinda yasa ba ya son fitowa yayi magana kada nan gaba a bada wani abu daga Gwamnati a ki rabawa dashi”

 

Zainab ta katseshi da cewa” Gwamnatin da zata kare?”

 

Jita ya kara da cewa ” Har uwargidan shugaban kasa ta fito ta yi magana amma ni inaga kamata yayi ta sameshi ta masa magana a sirri”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.