Tsohon na hannun damar shugaban kasa, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa nasara daya da jam’iyyar APC ta samu a mulkinta itace ta daina dorawa PDP Alhakin gazawarta.
Galadima ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Channelstv. Yace kowa zai iya fadin Abinda yake so tunda mulkin Dimokradiyya ake.
Yace amma shi a iya saninsa Nasara 1 tilo da APC ta samu shine ta daina dorawa PDP Alhakin zawarta.