fbpx
Sunday, December 4
Shadow

“Nasha shekaruna 74 amma sai aka cemin nakai 75″>>Inji shugaba Buhari

Da yammacin yaune shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin wata tawaga da ministan Abuja Muhammad Bello yawa jagora zuwa fadar shugaban inda sukaje sumai gaisuwar bangirma ta kirsimeti, da yake godewa bakin nashi, shugaba Buhari ya bayyana cewa, yaji dadin ziyarar da suka kawo mishi.

Ya kuma bayyana cewa wannan shekarar ta 2017, ansha gwagwarmaya, dan shi ya zatama shekarunshi saba’in da hudu amma sai akacemai ai yakai shekaru saba’in da biyar, ya kara da cewa rashinlafiyar da yayi ta jigatashi sosai dan baitaba yin irin wannan rashin lafiyarba, yace koda a lokacin yakin basasa da ya rika tuntube da kunyar rogo data doya bai sha irin wahalar da ya sha ta wannan ciwon ba.
Amma yace ya gode Allah saboda gashi ya wartsake, duk wanda ya sanshi lokacin daya dawo daga jiyya da kuma yanzu yasan ya kara samun lafiya sosai.
Shugaba Buhari yace sirrin samun lafiyarshi shine biyayyar da ya yiwa umarnin likitoci, yace shi sojane, shi ke bayar da umarni amma yanzu abu ya canja shi ake baiwa umarni, yace likitocinshi sun gayamai cewa yaci abinci kuma ya rika yin bacci sosai, kuma yayi hakan.
A karshe shugaba Buhari yace yaji dadain ziyarar da bakin suka kawomai saboda yana girmama makocinshi, shiyasama yana hawa mulki kasashen daya fara ziyara sune Chadi, Nijar, Benin da Kamaru, ya kara da cewa idan kana zaune da makwautanka lafiya, zaka zauna cikin kwanciyar hankali ka samu cigaba, amma idan ba zaman lafiya da makwaucinka to akwai matsala, shiyasa yake girmama makwautanshi na mutane da na kasashe.
Shugaba Buhari yace tabbas asha gwagwarmaya a shekarar 2017 amma yana fatan za’a samu cigaba da jin dadai a shekara me kamawa idan Allah ya kaimu.
Jaridar Punch. 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Karanta wannan  Aisha Buhari ta janye kararda ta kai Aminu Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *