Sunday, November 3
Shadow

Nasiha zuwa ga budurwa

‘Yan mata adon gari, kin taso kin fara kwalliya kina son ki yi saurayi, ko kumama kin taba yi, ga wasu nasihohi da zasu amfaneki idan kika yi Amfani dasu Insha Allah:

Babu namiji dake sonki fiye da mahaifinki, Mahaifinki ya fi kowa sonki a Duniya, Dan haka kada ki biyewa rudin saurayi yasa ki ki aikata abinda ba daidai ba saboda kina tsoron karki saba masa, idan ya rabu dake insha Allahu zaki hadu da wani me sonki.

Mahaifiyarki ta fi kowace mace sonki a Duniya: Hakanan kada rudin soyayya yasa ki biyewa saurayi ku aikata abinda ba daidai ba ko yasa ki sabawa Allah ko Iyayenki saboda tsoron karki rabu dashi, ki mai Nasiha, idan yaki, kada ki biye masa, ga soyayya ta gaskiya nan a gurin iyayenki mahaifi da mahaifiya.

Ka da ki yadda da kalmar Bazan barki ba ta saurayi: Duk da ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai samari masu amana amma baau da yawa, dan haka a lokacin da saurayinki ya ce miki ba zai barki ba, ki yadda dashi dan ana son yiwa mutane kyakkyawan zato, amma ki yi kaffa-kaffa.

Karanta Wannan  Nasiha ga masoyiyata

Yin Saurayi fiye da daya ba laifi bane: Idan dai ba an saka miki rana dashi ba ko mahaifinki yace ya bashi ke ba, yin saurayi fiye da daya ba laifi bane har sai an tabbatar an bashi ke, kai ko da an bashi ke ya kai kudi, idan wani ya ganki yana sonki, yana iya zuwa ya samu wanda zaki aura din, idan zai iya, yace masa ya bar mishi ke, yana so, idan ya yadda shikenan sai a mayar masa da kudinsa, ki auri sabon saurayin.

Idan zaki iya, kada ki tambayi saurayi komai, dalili kuwa shine a yayin da kika tambayi saurayi kudi, idan ba me tsoron Allah bane, shima ya samu kofar da zai tambayeki wani abu, ko ya nemi yin fasikanci dake, dan haka ki kiyayi tambayar saurayi kudi. Ki tambayi mahaifi, mahaifiya ko dan uwa na jini.

Karanta Wannan  Addu'ar janyo hankalin saurayi

Ka da ki yadda ko da wasa ki dauki bidiyon jikinki tsirara ki aikawa saurayi duk kuwa da irin son da yake miki ko kike mishi, ko da kuwa ana gobe aurenku ne. Komai zai iya faruwa.

Ki kiyayi yin samari ta yanar gizo wanda baki taba ganinsu a zahiri ba basu taba ganinki a zahiri ba, zasu iya miki karyar suna da hanyar hadaki da manyan masu kudi ko ‘yan siyasa su hure miki kunne ki aika musu Bidiyon ki tsirara, ina mai tabbatar miki karya suke. Zasu yi amfani da wannan bidiyon naki su rika miki barazana kina biya musu bukatarsu.

Karanta Wannan  YANZU - YANZU: Matashin Malami mai da’awah, Mufti Yaks ya rasú

Duk kawa ko aboki da kika yi a yanar gizo kada ki taba yadda dashi sai kun hadu gaba da gaba.

Kada ki yiwa saurayi dariya ya taba jikinki, idan yayi sau daya ki gaya masa baki so ya daina, ki nuna masa bacin ranki idan yaki, ki daina kulashi.

Kada ki sauya kaya ko ki yi tsirara a gaban koda kawayenki ne, ki sirrinta kanki, kada kiyadda mace ‘yar uwarki ta rika taba miki mazaunai ko nono da sunan wasa, ki ce mata bakya so.

Ki samu sana’a ko aikin yi, ki tambayi mahaifinki ya baki jari ki fara sana’a koda a cikin gidane ko da a yanar gizo ne.

Ki maida hankali a wajan karatunki na boko dana arabi sosai ki rika yin zarra a ajinku, zaki iya zama gwana kuma ki samu daukaka wadda baki tsammani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *