fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Naziru, Sarkin Waka dan neman sunane, jira yake kawai yaga wani abu ya yi ta maganganu na shirme, in ya isa ya fadi da wa yake>>Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa, tauraron mawakin Hausa, Nazir Ahmad Sarkin Waka dan neman sunane.

 

Hakan na zuwa ne bayan da ya mayar da martani kan kiran da Nafisar ta yi na cewa a daina haihuwar yara ana barinsu a titi suna zama Almajirai.

 

Maganar ta Nafisa duk da wasu sun yaba mata amma wasu da yawa sun yi Allah wadai da ita.

 

Nazir Sarkin Waka a nasa martanin, ya fadi cewa, ba Almajirai ne iyayen su suka haifesu suka kasa kula dasu ba, idan kana neman ‘ya’yan da iyayen su suka haifa suka kasa kula dasu ro ka taho masana’ntar fim.

 

 

Duk da yake bai kira Suna ba, wannan martani ne kai tsaye ga Nafisa, wadda ita kuma ta mayar masa da martanin cewa, dan neman sunane, ya kamata ya bugi kirji ya kira sunan da wa yake.

Karanta wannan  Da Dumi Dumi: Shugaban karamar hukumar mahaifar Atiku Abubakar ya koma jam'iyyar NNPP

 

Ta kara da cewa, shima fa Nazir dinnan dan fim ne.

 

Tace amma jira yake ya samu dama sai ya rika maganganin shirme.

 

 

Wannan lamadai na ci gaba da daukar hankula a shafukan sada zumunta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.