Hukumar kula da harkar sadarwa ta kasa, NCC ta ki amincewa da bukatar kamfanonin sadarwa da suka mika mata na kara kudin kira da aika sako hadda ma na data zuwa kaso 40 cikin 100.
Hukumar tace irin wannan kari ya kamata ya zama bai takurawa masu amfani da wayoyi ba sannan ya zamar da habakar kasuwanci yanda ya kamata.
Hukumar ta baiwa ‘yan Najeriya baki cewa, kada a tayar da hankula dan bata amince da karin kudin da kamfanonin sadarwar suka aike mata ba.
Kamfanonin sadarwar dai sun bukaci yin karin kudinne saboda yanda sukace suna kashe kudi sosai wajan gudanar da ayyukansu.