Friday, May 29
Shadow

NCDC ta samu gagarumar nasara a yaki da Coronavirus/COVID-19 inda zata fara kera abin gwajin Cutar

Hukumar kula da cututtuka ta Najeriya,  NCDC a takaice ta bayyana cewa ta samu gagarumar nasara a yakin da take da cutar Coronavirus/COVID-19.

Inda tace a yanzu ta samar da wani makamashi na musamman wanda zai bata damar samar da abin gwajin cutar Coronavirus cikin sauki yanda hakan zai bada damar awa mutane da yawa gwaji a Najeriya.

 

An yi gwajinne a a dakin gwaji na kasa, NABDA dake babban birnin tarayya, Abuja a jiya, Alhamis.

 

Shugaban hukumar kwararrun masu gwaji na kasa, Farfesa Alex Akpan ne ya shaidawa kamfanin dillancin Labaran Najeriya haka.

 

Yace wannan nasara da suka yi zata basu damar samar da abin gwaji a Najeriya cikin farashi me sauki wanda zai taimakawa Najeriyar dama wasu sauran kasashen Africa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *