Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama hodar iblis da aka ɓoye a tayoyin injinin cirar ciyayi guda 12 da aka shigo da su a ƙasar ta tashar jirgin sama a Fatakwal.
Hukumar ta ce wani mai suna Okechukwu Francis Amaechi, aka kama da hodar iblis wanda ya dawo daga Brazil.
Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an taba kama shi aka yanke masa hukunci a Brazil. Kuma ya dawo Najeriya ne bayan ya kama zaman gidan yari.
Hukumar ta kuma ce ta kama kwayar Tramadol 37,876 da kwalaben kodin 10,884 da taba wiwi kilo 825.016 a jihohin Zamfara da Kogi da River da Kaduna da kuma Kano