fbpx
Friday, March 31
Shadow

NDLEA ta kama kasurgumin mai safarar kwayoyin da ake zargi da alaka da Abba Kyari

Hukumar NDLEA da ke yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta ce ta kama wani kasurgumin mai safarar miyagun kwayoyi da ke da alaka da DSP Abba Kyari, dan sandan da aka dakatar daga aiki bisa zargin rashawa.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Litinin, ta ce jami’anta sun kama Cif Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wanda shi ne shugaban kamfanin Mallinson Group, bisa safarar tramadol ta naira biliyan uku.

Sanarwar, wacce kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya sanya wa hannu ta ce an kama Mr Ukata ne a filin jirgin saman Legas a kan hanyarsa ta tafiya Abuja.

“Bayan ya kwashe wata da watanni yana zille wa kamu, an kama Ukata, wanda shi ne shugaban rukunun kamfanonin Mallinson Group, a filin jirgin saman Lagos da ke Ikeja a cikin jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa Abuja ranar 13 ga watan Afrilu,” in ji sanarwar.

NDLEA ta ce Ukata yana da kamfanonin yin magunguna da kuma na robobi da yake amfani da su wajen yin safarar miyagun kwayoyi.

“Mun soma sanya idanu a kan Ukata ne a shekarar da ta gabata, bayan an kwace katon biyar na tramadol mai nauyin kilogiram 225 daga wurin wani ma’aikatansa ranar 4 ga watam Mayun 2021 lokacin da ya sayar da ita ga ‘yan sandan bad-da-kama na rundunar IRT da Kyari yake jagoranta a Ikeja da ke Lagos,” a cewar Babafemi.

Ya kara da cewa bayana kama ma’aikatan Ukata ne, suka kai yaran Abba Kyari wurin da yake ajiye kwayoyi inda suka kwace kwayoyin da kudinsu ya kai biliyan uku.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *