Saturday, July 13
Shadow

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi da aka shigar da su Najeriya daga India

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya, NDLEA ta ce jami’an ta sun kama kwalba 175,000 ta miyagun ƙwayoyi da maganin tari da aka shigar da su ƙasar daga India.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce sun yi wannan nasarar ne mako guda bayan wata irin ta da suka samu, inda suka kama hodar ibilis da aka shiga da ita Najeriyar, a jihar Rivers.

Ya yi bayanin cewa NDLEA da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro ta yi nasarar kama kayan laifin ne a ranar juma’a, 7 ga watan Yunin bana, bayan sun nemi gudanar da cikakken bincike a kan kayan da aka shigo dasu daga ƙasashen waje.

Karanta Wannan  'Matsalar Najeriya sai a ce ka cancanta amma ba ka da kuɗi'

Babafemi ya kuma bayyana cewa akwai sauran kayan laifi da suka haɗa ga kƙwaya da tabar wiwi da hodar ibilis da jami’an NDLEA suka kama a sassan Najeriya, a cikin makon da ya gabata.

Ya ce daga cikin kayan laifin da suka kama, akwai waɗanda aka shigo dasu daga ƙasashen waje da kuma waɗanda aka nemi fita dasu daga Najeriya zuwa ƙasashen wajen.

Hukumar NDLEA ta ce ba zata gajiya ba, a aikin da take yi na kawar da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *