fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Neman Shawara: Inason Mijina ya sakeni saboda komai sai yace in nema wajan uwargidansa

Wannan Rayuwa😭😭

Bayan kammala shirin MARAYU na karfe 4pm VisionFm92.5 Kano, na fito zan tafi gida, sai aka ce akwai wata mata tana jira na a qasa, ina zuwa naganta matashiya ce ba ta wuce 35yrs ba, amma wahala duk ya kodar da ita, ga wani hijab duk ya tsufa, takalminta ma daya yafi daya kokewa😣, na je nai mata sallama, na ce ‘ga ni’

Sai ta fara min bayani, “na zo wurin ki ya kai sau 4 ba mu hadu ba sai yau, ni da kike gani na marainiya ce, Baban mu ya mutu, lokacin da yake raye, na sha tsangawama a wurin ‘yan-uwana da muke UBA daya, sbd Suna cewa wai ni BA ‘YAR MAHAIFINA ba ce, ga shi ni kadai babata ta Haifa, kuma ta fita daga gidan, haka na sha azaba da tsangwama, ko da aka zo rabon Gado, cewa sukai ba zaa raba da ni ba wai ni ba ‘yar sa ba ce, sai da mai unguwa, dagaci da sauran tsofaffin unguwa suka sa baki tukun aka ban gad😭😭, na yi Aure, yara na 2 auren ya mutu, na koma gidan mu da zama, daga baya tsangwama ta dao sabuwa, Yanzu in taqaice miki, sun ce in bar musu gida ai an raba Gado don haka ban da hurumin zama a wannan gidan😭

Karanta wannan  So makaho ne: Wata matashiya 'yar shekara 15 ta yiwa kanta allurar jinin sahibinta mai dauke da cutar kanjamau

Na hada kayana, na je gun mamata, amma wlh aurenta sai da yai rawa dalilin zamana gun ta, shiyasa na haqura na bar gunta, na koma yawon gidajen ‘yan-uwa, abin ba zai yiwu ba wlh, sbd walaqancin da nke fuskanta, na nemi aikatau ban samu ba”

Saboda kar maganar tay yawa sai kawai na katse ta nace me kike so? sai ta ce ‘ so nk ku nema min taymako a Gina min ko daki daya na LANGA LANGA ne a fili na, na ce toh ki tafi Monday ki dawo, sbd yau mun gama na yau, tace toh ta tafi, sai dai bayan kamar 30m na fita sai ganin ta nai a cen nesa da office din, tana zaune ta hada kai da gwiwa tana ta kuka, na tsayar da me Napep dina nace ‘Hajia lapia, kawai sai cewa tay KUDIN NAWA BA ZAI KAI NI GIDA BA HAMSIN CE😭😭😭, na ce ta shigo mu sauketa, muka sauke ta, na bata abinda Allah ya hore min, da niyyar litinin ta dawo.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.