fbpx
Tuesday, May 24
Shadow

NERC ta musanta amincewa da ƙarin kuɗin wutar lantarki

Sanusi Garba, Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa, NERC, ya ce hukumar ba ta amince da wani sabon karin farashin kudin fito ba a ‘yan kwanakin nan.

Garba ya shaida wa manema labarai a Abuja a yau Juma’a cewa tun a 31 ga watan Disamba, 2021 a ka amince da yin kwaskwarima a kan kuɗin wuta kuma ya fara aiki a watan Fabrairun 2022.

“Ina so a madadin hukumar NERC, in bayyana karara cewa ya zuwa yau, ba mu amince da wani ƙarin farashin wutar lantarki ba, kuma babu wata alama da ke nuna cewa Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) za su ƙara farashin sa.

“Idan kun lura cewa farashin da kuke siyan wuta a cikin makonni ɗaya zuwa uku da suka gabata ya ƙaru, muna son mu ga shaida. Bayanin da aka buga a shafin yanar gizon NERC ai farashin da aka yi wa kwaskwarima ne a watan Disamba 2021.

Karanta wannan  Dan Gidan Ango Abdullahi Ya Lashe Zaben Fidda Gwani Duk Da Yana Tsare A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

“Aikinmu shine amincewa da neman ƙarin kuɗin wuta, kuma har yanzu ba mu samu an kawo mana ko ɗaya ba.

“Mun bayyana a fili cewa muna da wajibcin doka don yin karamin bita kowane watanni shida don kula da hauhawar farashin kayayyaki, canjin kuɗaɗen kasashen waje, da sauransu,” in ji shi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.