fbpx
Wednesday, October 21
Shadow

Newcastle1-4 Manchester United: Yayin da Bruno Fernandez ya barar da penariti karo na farko tun komawar shi Manchester

Manchester United tayi nasarar zira kwallaye uku ana daf da tashi wasan ta hannun Bruno Fernandez Aaron wan Bissaka da kuma Marcus Rashford wanda hakan yasa tayi nasarar lashe gabadaya maki uku da wasan bayan Harry Maguire ya zira tashi kwallon tun kafin aje hutun rabin lokaci.

Bruno Fernandez ya barar da penariti karo na farko tun komawar shi kungiyar Manchester United a watan janairu kuma yayi nasarar cin penaritin har guda goma a cikin guda 11 daya bugawa kungiyar. Dan wasan Portugal din yayi nasarar zirawa United kwallo a gabadaya wasannin ta guda uku da suka gabata sannan yaci kwallye 11 kuma ya taimaka wurin cin kwallye 8 a gabadaya wasanni 18 daya bugawa Manchester.
Newcastle ne suka fara jagorantar wasan bayan dan wasan Manchester Luke Shaw yayi kuskuren zira masu kwallo guda a minti na biyu da fara wasan kafin Maguire ya ramawa United kwallon cikin mintina 21. Aaron Wan Bissaka ya zamo dan wasan na 166 na daban daya zirawa Manchester United kwallo a gasar Premier League yayin daya ke buga wasan na 38 a yau.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *