Sunday, June 7
Shadow

Neymar ya bayar da tallafin dala miliyan daya don ayi amfani dasu wajen yaki da cutar coronavirus

An samu labari daga sun sport cewa Neymar ya bayar da tallafin miliyan biyar a kudin Brazil Wanda yake dai-dai da dala miliyan 1.5 don a yaki cutar coronavirus wadda ta dauke rayukan mutane har guda 50,000 a fadin duniya.

 

 

Dan wasan Brazil din mai shekaru 28 ya bayar da kudaden ne ga asusun UNICEF don ayi amfani dasu wajen lura da kuma yima mutanen dake dauke da cutar magani.
Tauraron Barcelona Lionel Messi shima ya bayar da taimako dala miliyan daya ga asibitoci don su cigaba da yiwa masu dauke da cutar magani. Mutanen duniya baki daya suna cikin fargaba tun da wannan annobar ta bayyana saboda yadda take saurin yaduwa a tsakanin al’umma da kuma yawan kisan da cutar take yi a fadin duniya.
Kasar Italia da Spain suna daya daga cikin mayan kasashen da cutar tafi kamari kuma an dakatar da gabadaya wasannin su. Kuma hakan yasa yan wasan juventus da manajan su sun yarda cewa zasu karbi ragin albashi na tsawon watanni hudu don su taimakawa kungiyar ta samu ragin euros miliyan 80.
Kuma ragin albashin da kungiyar zata yi zai fi shafar Cristiano Ronaldo ayayin da zai rasa sama da euros miliyan 9 daga cikin albashin shi.
An samu labari cewa dan wasan gaba na kungiyar juventus mendes shima ya bayar da kayan aiki ga asibiti dake sao joao a kasar Portugal.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *