Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Paris Saint Germain, Neymar ya bayyana ‘yan wasa guda biyar da suka fi shi kwarewa a harkar tamola.
Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manem labarai, inda yace masu da kyar ya iya amsa tambayar domi shima yana daya daga cikin zakarun ‘yan wasan tamola a wannan karnin.
Amma yace ‘yan wasa biyar da suka fi shi sun hada da Eden Hazard, Lionel Messi, Marco Veratti, Kevin De Bruyne da kuma Thaigo Alcantara.
Abin mamaki bai saka sunan abokinsa na kungiyar PSG ba watau Mbappe wanda ya kasance daya daga cikin zakarun ‘yan wasan tamola.