fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Neymar ya musanta cewa be killace kansa kan Coronavirus/COVID-19 ba

Neymar ya karyata cewa shi bai karya dokar da aka sa ta yin nesa da mutane ba daya koma kasar shi ta Brazil alhalin ya saka hotunan shi a shafin shi na Instagram tare da abokan shi suna buga wasan raga (volley ball).

Dan wasan mai shekaru 28 yace mutanen da yayi hotunan da su dama tare suka tafi daga Paris a jirgi izuwa kasar Brazil kuma suna killace kansu tare da shi ne.Kuma ya Kara da cewa yana cigaba da motsa jikin ne kamar yadda ya saba.
Mai magana da yawun Neymar yace: Neymar ya gayyaci wa’yanan mutanen ne don su killace kansu na tsawon kwanaki 14 kafin su tafi wajen iyalan su. Kuma ya Kara da cewa yaron shi Davi luka ne kadai ya ziyarce shi ayayin da yake killace kanshi amma ya guji sauran iyalan shi harda mahaifiyar shi da yar uwar shi da kakar shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Manchester United zata dauki Casemiro daga Real Madrid

Leave a Reply

Your email address will not be published.