fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Neymar ya tsorata da Najeriya:”Na ji dadin rashin haduwa da Najeriya a Rasha”>>injishi

media
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


Dan wasan Brazil Neymar Da Silva ya bayyana farin cikinsa na rashin hada kasarsa da Najeriya a cikin rukuni guda a gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a badi.
A lokacin da ya ke bayyana ra’ayinsa game da jadawalin da aka fitar a ranar Juma’a a birnin Moscow, Neymar wanda ke taka leda a PSG ta Faransa ya ce, wani sauki ne suka samu kan yadda suka yi sa’ar kaucewa haduwa da Najeriya da wasu kasashen Afrika a matakin rukuni.
A cewar Neymar, ‘yan wasan Afrika na nuna karfi sosai a yayin kokarin karbe kwallo daga abokan hamayya kuma sun cika gudu.
Brazil dai ta fada rukuni guda ne da Serbia da Costa Rica da Switzerland, yayin da da Najeriya ta fada rukunin Argentina da Croatia da Iceland.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Hotuna:Dalibin Jami'ar ABU yace ya hakura da karatun digiri da yake saboda kisan sa akawa Deborah da tawa Annabi Muhammad(SAW) batanci

Leave a Reply

Your email address will not be published.