by hutudole
Tauraron dan wasan kasar Brazil dake taka leda a kungiyar Paris Saint German, Neymar ya shirya hada bikin murnar shiga sabuwar shekara a kasar shi ta Brazil.
Neymar zai hada bikin ne a gidan shi wanda mutane kusan 150 zasu hallata duk da cewa ana tsaka da cutar sarkewar numfashi a cewar manema labarai na Goal.
Rahoton ya kara da cewa kamfanin Agencia Fabrica ne zasu tsara bikin kuma sun bayyana cewa za’a gudanar da bikin ne tare da bin tsauraran matakan kariya na lafiya dama gwamnati baki daya.