fbpx
Saturday, August 8
Shadow

Ni da iyalina za mu yi Sallar Idi a gida>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu ya ce shi da iyalinsa za su yi Sallah Idi a gida.

A sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a, ya ambato Shugaba Buhari yana cewa zai yi Salar Idi a gidan ne domin yin biyayya ga umarnin da Sarkin Musulmi ya bayar cea kowa ya yi sallar Idi a gida.

“Na dauki matakin ne bisa umarnin da Sultan na Sokoto kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bayar na dakatar da yin sallar Idi a kasa baki daya, ” a cewar Shugaba Buhari.

Saidai a wannan karin shugaban ba zai karbi gaisuwar Sallah kamar yanda aka saba yi a baya ba daga masu rike da mukaman siyasa da shuwagabannin al’umma ba, kamar yanda sanarwar ta bayyana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *