fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Ni dai nan da watanni 17 zan sauka daga Mulki amma fatana shine duk shugaban kasar da zai hau yayi abinda nayi kokarin yi na samar da tsaro>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa mutanen dake kashe juna a Arewa maso yamma mutanene guda masu al’ada iri daya.

 

Shugaban ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai jihar Borno inda ya bayyana cewa, sun samu gagarumar nasara a jihar.

 

Sannan kuma shugaban yace, amma akwai kalubale musamman daga yankin da ya fito na Arewa maso yamma.

 

Yace amma yayi odar makamai daga kasar Amurka da zai yi amfani dasu wajen yakar ‘yan Bindigar.

 

Shugaban ya kara da cewa, yayi rantsuwa da qur’ani a yayin da ya hau mulki cewa zai yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya biyayya.

 

Yace kuma nan da watanni 17 zai sauka daga Mulki. Dan hakane ma yake fatan duk wanda zai zama shugaban kasa ya dira, yayi qbinda shi yaso yi na samar da tsaro a Najeriya.

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada Aliko Dangote a matsayin shugaban sabuwar kungiyar da zata kawo karshen cutar Malaria a Najeriya

“I know and I swear with the Holy Quran, which I believe with that I will uphold the Constitution of the country, by that I must go in 17 months time, and I will go, God willing, and I hope whoever is coming will try to do the three things I tried to do. One, secure the country because unless the country is secured, it cannot be managed.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.