Mawallafin jaridar Ovation Magazine, Dele Momodu yace yasan ba zai iya ja da Atiku Abubakar da Gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ba wajan wasa da kudi.
Dele Momodu ya bayyana hakane a yayin da shima yake cikin masu neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.
Saidai yace yana da tasa dabarar da zai yi amfani da ita wajan yin nasara.
Dele Momodu ya bayyana hakane yayin da ake kara tunkarar zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP din.