Dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar AAC, Omoloye Sowore ya bayyana cewa shi zai lashe gabadaya kuru’un Kano akan sauran abokan takararsa a zaben 2023.
Ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya Abuja, inda ya gabatar da abokin takararsa Hatuna Magashi.
Kuma yace jam’iyyar shi ce zata yi nasarar lashe zaben shekarar 2023 saboda PDP da APC sun gaza a mulkin su.
A karshe yace Haruna Magashi zai taimaka masa wurin lashe kuru’un jihar Kano, kuma shi baya jin Peter Obi saboda ba’a san shi a jihar Kano ba.