fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ni zan gaji Buhari a 2023>>Fasto Tunde Bakare

Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa shine zai gaji shugaban kasa,Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

 

Ya bayyana hakane a hirarsa da Jaridar Sun, kamar yanda Hutudole ya samo, saidai bai bayyana jam’iyyar da zai fito takara ba inda yace sai nan da wani lokaci sannan za’a sani.

Ya kuma yi magana akan tsarin karba-karba inda yace ba lallai bane a ra’ayinsa duk wanda ya cancanta kawai ya zama shugaba ba sai an yi wata karba-karba ba.

 

Da aka tambayeshi me zai ce kan mulkin shugaba Buhari? Sai yace duk da dai ba’a kai inda ake son kaiwa ba amma shugaban yayi kokari sosai. Ta fannin tsaro da tattalin arziki.

Karanta wannan  Shugaban Hukumar zabe yayi tsokaci akan rahotannin dake bayyana cewa sun bude wuraren yin rigistar katin zabe a kasashen waje

 

An kuma Tambayeshi maganar Bola Ahmad Tinubu da shima watakila zai tsaya takarar shugaban kasa. Tunde Bakare yace yana masa fatan Alheri domin dan siyasa ne na gari.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.