Tauraron dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa shifa bai tursasa kungiyar dole sai ta sayar dashi a wannan kakar ba.
Ya bayyana hakan ne biyo bayan rahotannin dake bayyana cewa ya tursasa Manchester United ta sayar dashi a wannan kakar.
A kwanakin baya tauraron dan wasan ya nemi kingiyar ta sayar dashi don bata cancanci buga gasar zakarun nahiyar turai ba a kaka mai zuwa.
Kuma har yanzu dai babu wata tsayayyar kungiyar dake son daukarsa.