fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Nifa dama nasan Buhari bazai sakawa dokar zabe hannu ba, kuma na yadda a fille min kai idan yayi>>Buba Galadima

Fitaccen dan siyasar nan na Najeriya Injiniya Buba Galadima ya ce dama ya san shugaban kasar Muhammadu Buhari ba zai taba amincewa ya sanya hannu kan ƙudurin dokar zaɓen ƙasar mai ƙunshe da tilasta tsarin fid da gwani na ‘yar tinƙe ba.

Ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da BBC Hausa yayin da ‘yan kasar suke ci gaba da ce-ce ku-ce a kan matakin da Shugaba Buhari ya dauka na ƙin sa hannun a kan ƙudurin dokar zaɓen.

Wani bangare na wasikar da shugaban ya aike wa Majalisar dokokin tarayya ya ce zaɓen ‘yar tinƙe a mazaɓu sama da 8,000 na Najeriya, zai sa a samu matukar karuwa a kuɗin aiwatar da zaɓen fid da gwani a tsakanin jam’iyyu.

Sai dai Injiniya Buba Galadima, wanda tsohon abokan siyasar Shugaba Buhari ne, ya ce shugaban ya ki sanya hannu kan kudurin dokar ne “saboda wasu dalilai na kashin kansa ba domin taimakon al’umma ba.”

“Matakin bai ba ni mamaki ba, domin dama na fada a kafofin yada labarai masu yawa cewa na amince a fille min kai idan har Buhari ya sa hannu kan wannan kudurin dokar,” in ji shi.

Da aka tambayi Buba Galadima dalilinsa na cewa Buhari ba zai sanya hannu kan kudurin dokar zaben ba, sai ya ce: “Akwai wasu cikin mukarraban Buhari da ke ganin idan aka samar da dokar zabe mai inganci, to ba za su iya yin magudin zabe ta hanyar murda tanade-tanaden dokar ba. Na biyu mukarraban nasa na gaya masa cewa ba suna cin zabe ba ne domin suna da yawan jama’a, sai dai domin suna da karfin gwamnati kawai. Suna da jami’an tsaro wadanda za su ba su damar murdawa da karya zaben a gaba.”

Buba Galadima ya ce fiye da shekara biyu ke nan da aka kammala aiki kan dokar zaben, amma Buhari ya ki amincewa da ita.

Ya kara da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba.

“Ko yanzu aka cire abin da ba sa so a cikin kudurin dokar, idan aka kai ma sa, zai sake dawo wa da shi ga majalisa.”

Da aka tambaye shi game da zargin da yake yi cewa makusantan Shugaba Buhari ne ke zuga shi, cewa zargin ba mai tushe ne ba, sai ya ce:

“In fa aka yi zabe sahihi, ni ina tabbatar wa al’ummar Najeriya cewa jam’iyyar APC ko kansila daya ba za ta taba ci ba a kasar nan. In kuma sun isa, su sa hannu a dokar zaben kamar yadda ta ke.”

Kan batun hanzarin da shugaban Najeriya ya bayar cewa jam’iyyun siyasa za su bukaci makudan kudade wajen gudanar da zabukan ‘yan tinke da kudurin dokar ya tanadar, Buba Gladima ya ce ba haka lamarin ya ke ba.

“Ba fa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ce z ata gudanar da zabukan nan ba, jam’iyyun siyasa ne. Iyaka INEC ta sa ido domin ta tabbatar da an bi ka’ida, an bi sharuddan yin zaben.”

Ya kuma ce babu wasu makudan kudaden da jam’iyyun za su bukata.

“Ina ganin kuna da mantuwa wallahi. Kun manta cewa ni a matsauina na babban sakataren jam’iyyar CPC na kasa, ni ne na fara bayar da shawara aka yi zaben ‘yar tinke, aka fito aka yi ta kashe-kashe, gwamnatoci su ka shiga ciki domin yamutsa abubuwa a jihohi irinsu Kano da Bauchi da Katsina da Kaduna? An manta wannan? Ai ni ne wanda ya fara tsara zaben ‘yar tinke.”

Ya ce wannan matakin zai shafi kima da martabar shugaba Buhari a idon ‘yan Najeriya.

“Ai ya fadi ba nauyi, tun da ai bai manta ba cewa ba kukan da ba mu yi ba a duniyar nan, a Najeriyar nan, har da zanga-zanga na a tabbatar da dokar zabe sahihiya yadda talakawa za su zabi wanda suke so. Ashe tun da ya hau tudun na tsira, shi yasa ya manta da dukkan wadannan abubuwan da yayi a baya?

Daga BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.