fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Nine Gwamna idan ba’a zageni ba wa za’a zaga>>Gwamnan Kaduna

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa da ya zo mulki ya tarar ana biyan wasu mutanen kudancin Kaduna kudi wai dan a zauna Lafiya.

 

Yace ya dakatar da bayar da wadannan kudi inda yace bashi da lokacinsu. Yace yawancinsu wanda suke wannan abu basu da aikin yi ko sana’a. Hutudole ya samo muku wannan magana ta Gwamnane daga hirar da yayi da gidan talabijin na Channelstv, kamar yanda wakilinmu ya bibiya.

Gwamnan yace wasu ne kawai suke zuwa su tayar da husuma dan su samu kudin tallafi daga gurare daban-daban. Yace shi bai yadda da haka ba, ya hadasu da jami’an a yi maganin kowanene duk matsayinsa yace basa jin tsoronshi. Hutudole ya fahimci cewa gwanan yace Maharan dake kai hari na satar shanu Fulani ne wanda sun mayar da abin sana’a.

Karanta wannan  Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Rivers ya tsallakw rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka kashe masa jami'in dake tsaron sa

 

Yace kuma suna kaiwa kowa hari, basa banbancewa, yace har ‘yan uwansu Fulani suna kai musu hari. Hutudole ya ruwaito cewa Gwamnan ya bayyana cewa mutanen kudancin Kaduna suna ganin duk wanda ba dan asalin yankin ba a matsayin bare. Yace duk Dan Najeriya na da ‘yancin zuwa ko ina a cikin kasa ya zauna kuma zai baiwa mutanen sa kariyar data kamata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.