fbpx
Friday, August 12
Shadow

Nima ina goyon bayan gwamna Matwallen Zamfara na cewa a ba talaka lasisin mallakar bindugu su rika kare kawunansu, cewar Shehu Sani

Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyana cewa yana goyon bayan gwamna Matawallen Zamfara na cewa talakawa su sayi bindugu su riga kare kawunansu.

Inda yace harin da ake kaiwa arewacin kasar nana kamari sosai kuma ana cigaba da kashe manoma babu dalili, sannan makaranta da wuraren bauta suma ana kai masu hari.

Gwamna Matawallen Zamfara ya bukaci kwamishinan jihar ya ba mutanen da suka cancanci mallakar bindugu lasisi don kare kanwunansu.

Amma kwamishinan yace hakan ya sabawa doka don sun haramtawa mutane mallakar bindugu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.