Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi ya bayyana cewa ya gayawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
Gwamnan ya bayyanawa ‘yan jarida hakane a fadar shugaban kasar bayan ganawar da suka yi.
Umahi yace shugaba Buhari ya bashi shawarar cewa yayi tuntuba sosai kamin yanke shawara.
A jiya ne dai shima Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, ya gayawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai tsaya takarar shugaban kasa a shekarar 2023 wanda hakan ya jawo cece-kuce.